Ranar Alhamis za a fara wasannin cike gurbi a Federation Cup a karawar maza da ta mata a Gombe da Jos da Katsina da kuma Enugu.
Bayan da aka kammala samun zakarun jihohi a makon jiya, hukumar kwallon kafa ta Nigeria ta samu kungiyoyi 70, masu fatan lashe kofin bana.
Sai dai jihar Yobe ba ta shiga gasar bana ba, yayin da jihar Borno da Adamawa kowacce ta yi wa kungiya daya rijistar fafatawa a Federation Cup na kakar nan – kenan an samu kungiya 70 maimako 74.
Cikin 70 dahga ciki an ware 12 da za su yi karawar cike gurbi da aka zakulo ta gwada kwazo tsakanin wadanda suka kai zagayen gaba, sannan 58 za su jira a gama fafatawar cike gurbi.
Za a fitar da shidan da za a hada su zama 64 daga nan ne za a raba jadawalin ci gaba da wasannin Federation Cup na 2024 a wasannin maza.
A bangaren mata kuwa an samu kungiya 31 daga ciki jihohi 20 suka yi rijista, yayin da jihar Benue, Ekiti, Imo, Kogi, Kwara, Nasarawa, Ogun, Osun da kuma Oyo kowacce take da kungiya daya.
Jihohin da suka yi wa kungiya biyu rijista kuwa a wasannin mata sun hada da Abia, Bayelsa, Delta, Edo, Enugu, Kaduna, Lagos, Ondo, Plateau, Rivers da kuma Aabuja, babban birnin tarayya.
Jadawalin wadanda za su yi karawar cike gurbi
. Classic FC (Adamawa) Vs Gamji Eaglets (Taraba) – Gombe – 4pm
. Warinje FC (Bauchi) Vs Simon Ben Academy (Kaduna – Jos – 4pm
. Zamfara United Feeders (Zamfara) Vs PRO Line (Kano) – Katsina – 4pm
. Ine Stars (Edo) Vs Crusaders FC (Bayelsa) – Asaba – 4pm
. KC FC (Kogi) Vs PCM FC (Ebonyi) – Enugu – 2pm
. Flight FC (Benue) Vs Fr. Eburuaja (Imo) – Enugu – 4pm
Kungiyoyi biyun da suke wakiltar jihohinsu
Abia State: Enyimba FC, Abia Warriors
Adamawa State: Classic FC
Akwa Ibom State: Akwa United, FC One Rocket
Anambra State: Solution FC, Edel FC
Bauchi State: Wikki Tourists, Warinje FC
Bayelsa State: Bayelsa United, Crusaders FC
Benue State: Lobi Stars, Flight FC
Borno State: El-Kanemi Warriors
Cross Rivers State: Rovers FC, May Frank FC
Delta State: Warri Wolves, Delta Marine FC
Ebonyi State: Cynosure FC, PCM FC
Edo State: Bendel Insurance, Ine Stars
Ekiti State: Ekiti United, Ekiti United Feeders
Enugu State: Rangers Int’l, Coal City FC
FCT: EFCC FC, Sporting Supreme FC
Gombe State: Gombe United, Doma United
Imo State: Ikukuoma FC, Fr. Eburuaja FC
Jigawa State: Lautai FC, Dutse Strikers
Kaduna State: Green Beret FC, Simon Ben Academy
Kano State: Kano Pillars, PRO Line FC
Katsina State: Katsina United FC, Jr. Danburan FC
Kebbi State: Discovery Talent Academy, Kebbi United
Kogi State: KC FC, FC Bako
Kwara State: Kwara United, ABS FC
Lagos State: Inter Lagos FC, Ikorodu City FC
Nasarawa State: Nasarawa United, FC Basira
Niger State: Niger Tornadoes, Niger Tornadoes Feeders
Ogun State: Beyond Limit FC, Stormers Sports Club
Ondo State: Sunshine Stars, Adanimogo FC
Osun State: Osun United, Hammola Int’l FC
Oyo State: Ilaji FC, Shooting Stars
Plateau State: Plateau United, Mighty Jets
Rivers State: Rivers United, Ofirima FC
Sokoto State: Sokoto United, Jedo Academy
Taraba State: Gamji Eaglets FC, Karim United
Zamfara State: Zamfara United, Zamfara United Feeders
Kungiyoyin da suke wakiltar jihohinsu a bangaren mata
Abia State: Abia Angels, Ahudiya Nnem Queens
Bayelsa State: Bayelsa Queens, GoldenSun Sports Club
Benue State: Honey Badgers
Delta State: Delta Queens, Delta Ladies
Edo State: Edo Queens, Fortress Ladies
Ekiti State: Ekiti Queens
Enugu State: Bright Future FC, Greenfoot FC
FCT: Naija Ratels, ON Youth Academy
Imo State: Heartland Queens
Kaduna State: Kada FC, Gallant FC
Kogi State: Confluence Queens
Kwara State: Kwara Ladies FC
Lagos State: FC Robo Queens, Dannaz Ladies
Nasarawa State: Nasarawa Amazons
Ogun State: Remo Stars Ladies
Ondo State: Sunshine Queens, Onimang FC
Osun State: Osun Babes
Oyo State: Suit De Queens
Plateau State: Plateau United Queens, Mighty Jets Int’l Mata
Rivers State: Rivers Angels, Oske Lean FC