An bayyana raflin wasan Real da Man City a Champions League

Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester City a Santiago Bernabeu a wasan quarter final a Champions League ranar Talata.

Tuni hukumar kwallon kafa ta turai ta nada alkalin wasan da zai busa wasan hamayya tsakanin Real mai Champions League 14 da City mai rike da kofin bara.

Dan kasar France François Letexier shi ne zai busa wasan tare da taimakon Cyrill Mugnier da Mehdi Rahmouni, kamar yadda UEFA ta sanar a karshen mako.

Wannan shi ne wasa na uku da Letexier zai busa wasan Real Madrid a Champions League.

Wasannin da Letexier ya busa wa Real a Champions League

  • Real Madrid 2-0 Chelsea (Quarter-final first wasan farko – Champions League 2022/23).
  • Real Madrid 4-2 Napoli (Wasa na biyar cikin rukuni – Champions League 2023/24)

Haka kuma Dan kasar Sweden, Glenn Nyberg zai yi alkalancin karawa tsakanin Arsenal da Bayern Munich tare da taimakon, Mahbod Beigi da kuma Andreas Soderqvist.

Nyberg shi ne alkali a karawar da Bayern ta doke Manchester United 4-3 a bana a cikin rukuni a Champions League.

Leave a comment