Messi ya ci kwallo a wasan farko bayan kammala jinya

Lionel Messi ya ci kwallo a wasan da Inter Miami ta tashi 2-2 da Colorado, wasan farko da kyaftin din Argentina ya buga bayan kammala jinya.

Tsohon dan wasan Barcelona bai yi wa Inter Miami wasa hudu ba sakamakon jinya, wanda aka saka shi a karawar ya canji dan wasa lokacin da ake cinsu 1-0.

Messi ne ya farke kwallon daga baya ya bai wa Leonardo Afonso ya zura na biyu a raga.

Miami za ta je Monterrey ranar Laraba a Concacaf Champions League quarter finals, bayan da aka doke ta a wasan farko 2-1 a kungiyar dake Mexico.

Leave a comment