Bayern ta yadda da Nagelsmann amma tana tuntabar wasu kocin

Bayern Munich ta sanar cewar ta gamsu da kwarewar kociyan tawagar Germany, Julian Nagelsman, domin maye gurbin Thomas Tuchel, amma tana tuntubar wasu masu horar da tamaula.

Tuchel ya sanar cewar zai ajiye aikin jan ragamar Bayern Munich a karshen kakar nan, bayan da Bundesliga ya sullube mata na kakar nan.

Bayern Leverkusen ce ta daya a Bundesloga da tazarar maki 16 tsakaninta da Bayern Munich ta biyu mai kofin bara.

A bara ne Bayern ta kori Nagelsmann cikin Maris din 2023, wanda ake cewa shi ne zai maye gurbin Tuchel, bayan da kwantiraginsa da tawagar Germany zai kare a karshen gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro 2024.

Germany za ta karbi bakuncin Euro 2024 daga Yuni zuwa Yulin 2024.

Kociyan da ya ja ragamar Bayern Munich fiye da kaka biyu a bayan nan shi ne Pep Guardiola daga 2013 zuwa 2016.

Bayyan Nagelsmann da ake cewa Bayern ta tuntuba, an kuma ce tana son gwada daukar kociyan Brighton, Roberto De Zerbi ko kuma na tawagar Austria, Ralf Rangnick.

Leave a comment