Leverkusen za ta lashe Bundesliga a karon farko a makon gaba

Bayer Leverkusen ta doke Union Berlin 1-0 ranar Asabar, za ta lashe Bundesliga na farko a tarihi a makon gaba da za ta karbi bakuncin Werder Bremen.

Florian Wirtz ne ya ci kwallon tun kan hutu a karawar da Berling ta kare da ‘yan wasa 10 a cikin fili, kenan Leverkusen mai jan ragamar teburin Bundesliga ta bai wa Bayern Munich ta biyu tazarar maki 16.

Ranar Asabar Bayern Munich, wadda ta kai ziyara Heindeinhem ta fara cin kwallo biyu a babbar gasar tamaula ta Germany daga baya aka farke aka kuma kara mata na uku.

Leverkusen wadda ta yi wasa 41 a bana ba a doke ta ba har da 28 a Bundesliga, tana da damar lashe kofin 2023/24 idan ta yi nasara a kan Bremen ranar Lahadi, koda Bayern Munich za ta yi nasara a kan Cologne ranar Aasabar.

Idan kuma Bayern Munich ta kasa cin Cologne ranar Asabar, kenan Leverkusen ta dauki Bundesliga na kakar tun kan wasan da za ta buga a gida kenan.

Leverkusen tana buga Bundesliga tun daga 1979, wadda ta lashe UEFA Cup a 1998 da German Cup a 1993, daga nan ba ta sake daukar wani babban kofi ba.

Kungiyar ta yi rashin nasara a wasan karshe a kofi daya da yin ta biyu a Bundesliga karo biyar, hakan ya sa ake kiranta da sunan Vizekusen (Vicekusen) a Germany a kuma duniya ake ce mata Neverkusen.

Leave a comment