Bayanai kan wasan Brighton da Arsenal a Premier

Arsenal za ta fafata da Brighton a wasan mako na 32 a Premier League ranar Asabar.

Gunners ta yi nasarar cin Brighton 2-0 a Emirates ranar 17 ga watan Disamba a wasan farko da suka yi a bana a gasar, inda Gabriel Jesus da Kai Havertz suka ci mata kwallayen.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool ta daya, ita kuwa Brighton mai maki 43 tana ta tara.

Rahoton kan wadanda ke jinya

Brighton za ta yi wasan ba tare da Adam Webster da Evan Ferguson, amma Valentin Barco da Ansu Fati sun murmure.

Har yanzu Kaoru Mitoma da Solly March da James Milner da Billy Gilmour na jinya.

Kocin Brighton, Roberto de Zerbi ya tabbatar cewar Bart Verbruggen ne zai tsare raga.

Ana auna koshin lafiyar Bukayo Saka, wanda bai yi wasan da Gunners ta ci Luton Town 2-0 ranar Laraba ba.

Za a fara karawar da Declan Rice, wanda ya fara da zaman benci daga baya aka saka shi a karawar da Arsenal ta doke Luton ranar Laraba.

Dan wasan da aka tabbatar yana jinya a Arsenal shi ne Jurrien Timber.

Bayanai da ya shafi wasa a tsakaninsu

Arsenal ba ta yi rashin nasara daga wasa uku baya da ta ziyarci Brighton ba, wanda ta ci karawa biyu da canjaras daya.

Kowacce ta yi nasara biyar daga fafatawa 13 a Premier League tsakanin Arsenal da Brighton.

Kungiyar Brighton

Ba a doke Brighton ba a wasa 14 a dukkan karawa da ta yi a gida ba, wadda ta ci fafatawa takwas da canjaras shida, tu daga watan Satumbar 2023.

Ta ci kwallo a kowanne wasa 16 a da fara lik a bana, daga nan ta kasa zura kwallo a raga a wasa daga 14.

Wasa uku Brighton ta ci daga 18 da ta buga da karfe 5:30 ranar Aasabar.

Danny Welbeck ya ci Arsenal kwallo a wasa hudu daga biyar a dukkan fafatawa.

Kungiyar Arsenal

Arsenal ta ci wasa tara daga 10 baya da ta kara a Premier League

Ta hada maki 28 daga 30 da yake kasa a lik a 2024 da cin kwallo 35 aka zura mata hudu a raga.

Ba a doke Arsenal ba daga karawa 39 idan ta fara cin kwallo kan hutu, ta lashe 36 daga ciki da canjaras uku.

Haka kuma ta yi nasara a wasa 15 idan ita take kan gaba bayan da aka koma zagaye na biyu.

Martin Odegaard ya ci kwallo biyu ya bayar da biyu aka zura a raga a Premier daga karawa shida da ya fuskanci Brighton.

Ben White na daf da buga wa Arsenal wasa na 100 a Premier League.

Leave a comment