Man United ta kafa tarihi biyu mai muni a wasa da Chelsea

Chelsea ta doke Manchester United 4-3 a wasan mako na 31 a Premier League a Stamford Bridge ranar Alhamis.

Wasa na 12 da ta yi rashin nasara a Premier League kuma na 17 a dukkan fafatawa, karon farko da rashin kwazo tun bayan 1989/90 kenan shekara 24.

A wancan lokacin United ta kare a mataki na 13 a rukunin farko lokacin ba a sauya fasalin gasar zuwa Premier League ba.

A wannan kakar bayan da aka ci United wasa 12 daga karawa 30 a Premier League, duk da haka tana fatan samun gurbin shiga gasar zakarun Turai ta bani, wadda ke fatan kammala gumurzun bana cikin ‘yan shidan teburi.

Sauran wasannin da aka doke United a kakar nan har da wanda Newcastle United ta yi waje da ita a League Cup da shan kashi a fafatawa hudu daga wasa shidan da ta yi a Champions League.

Daya tarihin mai muna shi ne United ce ke kan gaba da cin kwallo 3-2 daga baya Chelsea ta farke ta kuma kara na uku a cikin karin lokacin da za a tashi daga fafatawar.

Wadda ta yi irin sakacin United ita ce Sheffield United a bana, wadda ta yi rashin nasara a hannun Tottenham, bayan ita ce kan gaba a minti na 98 daga baya aka farke aka kuma doke ta.

A wasan na Tottenham Dejan Kulusevki ne ya ci kwallon da ya bai wa kungiyarsa maki uku a minti na (99:53) shi kuwa Palmer ya zura na shi a ragar United a minti na 100:39.

Ranar Lahadi Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 32 a Premier League, bayan da suka tashi ba ci 17 ga watan Disambar 2023.

United ce ta yi waje da Liverpool a FA Cup na bana da cin 4-3.

Leave a comment