Palmer ya zama na farko a Chelsea da ya ci fenariti 7 a kaka daya a Premier

Chelsea ta yi nasarar cin Manchester United 4-3 a wasan mako na 31 a gasar Premier League ranar Alhamis a Stamford Bridge.

Kungiyar da Mauricio Pochettino ke jan ragama ta fara cin kwallo ta hannun Conor Gallagher daga baya Cole Palmer ya ci uku rigis, kuma biyu a bugun fenariti.

Haka kuma Palmer ya zama matashi na biyu a tarihin Premier mai shekara 21 da kwana 334 da ya ci fenariti biyu a wasa daya, wanda ke rike da bajintar shi ne Mario Balotelli a Disambar 2010 lokacin da Man City ta doke Aston Villa yana da shekara 20 da kwana 138 a lokacin.

Kenan Palmer ya zama na farko da ya ci fenariti bakwai a Chelsea a kaka daya ta Premier League.

Manchester United kuwa ta zura kwallo uku a raga ta hannun Bruno Fernandes da kuma Alejandro Garnacho da ya ci biyu a wasan na hamayya a babbar gasar tamaula ta England.

Kungiyoyin da Palmer ya ci a bugun fenariti a bana

  • Burnley kwallo daya ranar 7 ga watan Oktoban 2023
  • Arsenal kwallo daya ranar 21 ga watan Oktoban 2023
  • Tottenham kwallo daya ranar 6 ga watan Nuwambar 2023
  • Manchester City kwallo daya ranar 12 ga watan Nuwambar 2023
  • Fulham kwallo daya ranar 13 ga watan Janairun 2024
  • Manchester United kwallo biyu ranar 4 ga watan Afirilun 2024

Wanda ke kan gaba a tarihin cin bugun daga kai sai mai tsaron raga a Premier League a kaka daya a Chelsea shi ne Frank Lampard mai 10 a kakar 2009/10 da kuma Jorginho mai bakwai a 2020/21.                  

Manchester United mai kwantan wasa tana da maki 48 a mataki na shida, ita kuwa Chelsea mai maki 43 ta yi sama zuwa matakin ta 10 mai kwantan wasa biyu.

Manchester United za ta buga karawar mako na 32 da karbar bakuncin Liverpool ranar Lahadi 7 ga watan Afirilu, a kuma ranar ce Chelsea za ta ziyarci Sheffield United.

Leave a comment