Leverkusen za ta kara da Kaiserslautern a wasan karshe a German Cup

Bayer Leverkusen za ta kece raini a wasan karshe a German Cup da Kaiserslautern, bayan da ta caskara Fortuna Dusseldorf 4-0 ranar Laraba a zagayen daf da karshe.

Tun cikin minti na 20 Leverkusen ta zura kwallaye a raga ta hannun Jeremie Frimpong da kuma Amine Adil, daga baya Florian Wirtz ya ci biyu a karawar daya daga ciki a bugun fenariti.

Rabonda Leverkusen wadda ke jan ragamar teburin Bundesliga ta lashe German Cup tun 1993, kuma babban kofi na karshe da ta dauka kenan tun daga lokacin.

Kaiserslautern ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi nasara a kan Saarbrucken 2-0 a daf da karshe da suka fafata ranar Talata.

Har yanzu ba a doke kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama a bana, wadda ke shirin lashe kofi uku a kakar nan.

Leverkusen tana jan ragamar teburin Bundesliga da tazarar maki 13, mai fatan daukar Bundesliga a karon farko a tarihi, wadda za ta kara da West Ham a zagayen daf da na kusa da na karshe a Europa League a cikin watan nan.

Leverkusen ta kai wasan karshe a DFB-Pokal a 2020, amma ta yi rashin nasara da ci 4-2 a hannun Bayern Munich.

Za a buga wasan karshe a German Cup ranar 25 ga watan Mayu a filin wasa na Olympiastadion a Berlin.

Leave a comment