Shin Liverpool za ta iya kado Arsenal daga mataki na daya a Premier?

Liverpool za ta fafata da Sheffield United a wasan mako na 31 a gasar Premier League ranar Alhamis a Aanfield.

Kungiyoyin biyu sun kara a bana ranar 6 ga watan Disambar 2023, inda Liverpool ta ci kwallo biyu a karawar ta hannun Virgil van Dijk da kuma Dominik Szoboszlai.

Liverpool na fatan komawa kan mataki na daya a kan teburin Premier League, matakin da Arsenal ke kai da tazarar maki daya tsakaninta da kungiyar Anfield, bayan da ta ci Luton Town 2-0 ranar Laraba a Emirates.

Sheffield United mai wasa 29 tana da maki 15, ita ce ta karshen teburi.

Bayanai da suka shafi koshin lafiyar ‘yan wasa

Ana sa ran Andy Robertson zai koma taka leda, bayan da ya ji rauni a karawa da Brighton, sai dai ana tantama kan koshin lafiyar Wataru Endo.

Sheffield United za ta je Anfield ba tare da George Baldock da kuma Tom Davies ba.

Mai ci wa kungiyar kwallaye, Cameron Archer na murmurwa, wanda ke fama da doguwar jinya.

Abinda ya shafi kungiyoyin biyu

Liverpool ta yi nasarar cin wasa shida baya da suka hadu a Lik, kuma kwallo daya ne ya shiga ragarta.

Wasan da Sheffield United ta yi nasara a kan Liverpool a baya nan a Anfield shi ne cikin Afirilun 1994.

A wasan farko da Chris Wilder ya ja ragamar ne, Liverpool ta je ta yi nasarar cin 2-0 cikin Disamba.

Kungiyar Liverpool

Wasa daya aka doke Liverpool daga 39 da ta fuskanci sabbin kungiyoyin da suka hau gasar Premier da canjaras shida da cin karawa 32.

Saura kwallo biyar ya rage Liverpool ta zura 700 a raga karkashin Jurgen Klopp.

Sauran wasannin da suka rage a kammala kakar bana, tuni Liverpool tana da maki 67, irin yawan wanda ta samu a bara kenan.

Liverpool ta yi karawa 27 a lik a Anfield ba tare da rashin nasara ba tun daga doke ta 2-1 da Leeds United ta yi a cikin Oktoban 2022.

Kungiyar Sheffield United

Wasa daya kacal Sheffield ta yi nasara a waje a bana, shi ne wanda ta je ta doke Luton 3-1.

Ben Brereton Diaz Villareal ya ci kwallo hudu daga karawa biyar, tun bayan da aka dauko aronsa a watan Janairu daga Villareal ta Spain.

Kawo yanzu an zura kwallo 77 a ragar Sheffield United a kakar nan.

Kungiyar da Wilder ke jan ragama ta fara cin kwallo biyu a karawa biyu daga baya aka farke su a karawa da Bournemouth da suka tashi 2-2 da wanda suka yi 3-3 da Fulham.

Leave a comment