Ko Man United za ta ci Chelsea gida da waje a bana?

Chelsea za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan mako na 31 a Premier League da za su kara ranar Alhamis a Stamford Bridge.

Ranar 6 ga watan Disambar 2023, United ta doke Chelsea 2-1 a Old Trafford, wadda ta ci kwallo biyu ta hannun Scott McTominay, inda Cole Palmer ya ci wa Chelsea daya.

United ma wasa 29 tana ta shidan teburi da maki 48, ita kuwa Chelsea mai maki 40 tana ta 12 mai fafatawa 28 a babbar gasar tamaula ta England.

Labarai da ya shafi kungiyoyin biyu

Da kyar ne idan dan wasan Chelsea, Ben Chilwell zai iya buga karawar, bayan da ya kamu da rashin lafiya, duk da yana jinya.

Mai tsaron baya,Trevoh Chalobah da Malo Gusto suna cikin koshin lafiya, yayin da Robert Sanchez ya murmure.

Wadanda ke jinya a Manchester United sun hada da Victor Lindelof da Lisandro Martinez.

Amad Diallo ya kammala hutun dakatarwar da aka yi masa, sakamakon jan katin da aka yi masa bayan murnar cin kwallo a karawa da Liverpool a FA Cup zagayen kwata fainals.

Abinda ya shafi karawa tsakanin kungiyoyin

Chelsea ba ta ci wasa ba daga 12 da ta kara a Premier League tsakaninta da United, mai canjaras bakwai da rashin nasara biyar

Chelsea ba ta yi nasara a kan United a babban wasa a gaban ‘yan kallo tun 1-0 da ta ci a Wembley a wasan karshe a FA Cup a 2018.

United na fatan doke Chelsea gida da waje a kakar tamaula daya tun bayan bajintar da ta yi a 2019/20.

Kungiyar Chelsea

Cikin wasa 15 da Chelsea ta buga a baya a dukkan fafatawa, Wolves ce ta doke ta a cikin Fabrairu, wadda ta ci karawa 10 da canjaras hudu.

An zura kwallo 47 a ragar Chelsea kawo yanzu a bana, irin yawan wadanda aka zura mata a kakar bara ta 2023/24.

Cole Palmer yana da hannu a ci wa Chelsea kwallo 21 a Premier League, wanda ya ci 13 ya bayar da takwas aka zura a raga.

Raheem Sterling ya kasa zura kwallo a ragar United a wasa 25 da ya fuskanci kungiyar Old Trafford a dukkan fafatawa.

Kungiyar Manchester United

Kawo yanzu an ci Manchester United a wasa 11 a Premier League a bana, saura daya ta yi kan-kan-kan da yawan wadanda aka doke ta a bara a 2022/23 – an ci United wasa 12 a kakar 2013-14 da kuma 2021-22.

Haka kuma wasa daya kacal ta yi nasara daga tara a Premier League da ta ziyarci kungiyoyin London, wadda aka doke a wasa hudu daga shida baya da ta kara.

Mason Mount ya ci wa United kwallo a karon farko a karshen mako da ta tashi canjaras da Brentford a fafatawa ta 14 da ya yiwa kungiyar.

Mount ya ci wa Chelsea kwallo 33 a wasa 195 a dukkan fafatawa tun bayan da ya koma Stamford Bridge daga baya ya koma United.

Leave a comment