Kaiserslautern ta taka wa FC Saarbrucken burki a German Cup

Kaiserslautern ta kawo karshen FC Saarbrucken wadda ta dade tana yin nasara a German Cup na bana, yanzu an fitar da ita a zagayen daf da karshe.

FC Saarbrucken, wadda ke buga gasa mai daraja ta uku a Germany, ita ce ta yi waje da Bayern Munich da Borussia Monchengladbach da kuma Eintracht Frankfurt a bana a DFB-Pokal..

An doke kungiyar da ci 2-0 ranar Talata, wadda aka zura mata kwallayen ta hannun Marlon Ritter da kuma Almamy Toure.

Ranar Laraba, wadda take ta daya a kan teburin Bundesliga Bayer Leverkusen za ta fuskanci Dusseldorf a daya karawar ta daf da karshe.

Wannan shi ne karon farko da Kaiserslautern ta kai wasan karshe a kofin tun bayan 2003, lokacin da Bayern Munich ta doke ta.

Leave a comment