Ronaldo ya ci kwallo uku rigis karo biyu a kwana hudu

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo uku rigis karo na biyu a kwana hudu, bayan da Al Nassr ta caskara Abha 8-0 ranar Talata a gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Tun kan hutu dan kwallon tawagar Portugal ya ci uku rigis da kuma Sadio Mane da ya ci daya a wasa.

Daf da hutu ne Al Nassr ta kara na biyar a raga ta hannun Abdulmajeed Al Sulaiheem.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Abdulrahman Ghareeb ya kara daya, sannan Abdulaziz Saud Al Aliwa ya zura biyu a raga a karawar.

Ranar Asabar tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus ya ci uku rigis a wasan da Al Nassr ta doke Al Tai 5-1.

Al Nassr, wadda take ta biyu a kan teburin babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia za ta je gidan Damac ranar Juma’a, domin buga fafatawar mako na 27.

Leave a comment