Ko Liverpool za ta kai ga lashe Premier League na bana?

Liverpool tana jan ragamar teburin Premier League, bayan da ta buga wasa 29 a kakar 2023/24.

Kungiyar Anfield tana ta daya da maki 67, sai Arsenal ta biyu da maki 65 da kuma Manchester City ta uku mai maki 64.

Ranar Lahadi aka raba maki tsakanin Manchester City da Arsenal a Etihad a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ita kuwa Liverpool cin Brighton 2-1 a dai ranar Lahadi a Anfield, kuma minti biyu da fara wasa Brighton ta fara cin kwallo ta hannun, Danny Welbeck.

Daga baya Liverpool ta farke ta hannun Luis Diaz, sannan Mohamed Salah ya kara na biyu da hakan ya bai wa Liverpool maki ukun da take bukata a fafatawar.

Karo na bakwai kenan a bana da ake fara cin Liverpool a bana daga baya ta farke, sannan ta lashe wasan.

Kenan ba a doke Liverpool ba a Anfield a wasa 28 baya a Premier League da ta fuskanci kungiyar da take cikin ‘yan goman farko.

Daga ciki ta yi nasara a fafawa 17 da canjaras 11 tun bayan da Chelsea ta doke ta 1-0 a Maris din 2021.

Ranar Alhamis, Liverpool mai kwantan wasa za ta karbi bakuncin Sheffeld United, ranar Laraba ne Arsenal mai kwantan wasa za ta yiwa Luton Town masauki a Emirates.

Itama Manchester City kwantai daya take da shi, wadda za ta je gidan Chelsea ranar Alhamis a wasan mako na 31 a babbar gasar tamaula ta England.

Wasannin mako na 31 da za a buga a Premier League

Talata 2 ga watan Afirilu 2024

  • Newcastle United da Everton    
  • Nottingham Forest da Fulham  
  • Burnley da Wolverhampton Wanderers             
  • Bournemouth da Crystal Palace
  • West Ham United da Tottenham

Laraba 3 Afirilu 2024

  • Arsenal da Luton Town 
  • Brentford da Brighton & Hove Albion    
  • Manchester City da Aston Villa 

Alhamis 4 Afirilu 2024

  • Liverpool da Sheffield United
    • Chelsea da Manchester United 

Leave a comment