Real Madrid za ta yi wasa biyar cikin Afirilu

Kungiyar Real Madrid za ta buga wasa biyar a cikin sabon watan Afirilun kakar bana, wadda take shirin lashe La Liga da Champions League.

Real din za ta fafata a wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League, inda za ta fara karbar bakuncin Manchester City, sannan ta je England a wasa na biyu a cikin watan.

Sauran wasa ukun da za ta kara a cikin Afirilu, za ta yi ne a La Liga, inda za ta fara da zuwa gidan Mallorca da na hamayya tsakaninta da Barcelona a Bernaeu da wanda za ta je Sociedad.

Real Madrid tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 75, sai Barcelona ta biyu mai maki 67 da kuma Girona 56 da maki 65 da Atletico Bilbao mai maki 56.

Real Madrid mai Champions League 14 jimilla ta fice daga gasar bara ta hannun kungiyar Etihad, bayan da suka tashi 1-1 a Spain, inda aka dpke Real 4-0 a England.

Hakan ya bai wa City damar zuwa ta lashw Champions League na 2022/23 kuma na farko a tarihi.

A kuma barar City ta hada da lashe FA Cup da kuma Premer League.

Wasa biyar da Real Madrid za ta yi a cikin watan Afirilu

Champions League Talata 9 ga watan Afirilu    

•            Real Madrid da Man City     

Spanish La Liga Asabar 13 ga watan Afirilu      

•            Mallorca da Real Madrid     

Champions League Laraba 17 ga watan Aafirilu    

•            Man City da Madrid     

Spanish La Liga Lahadi 21 ga watan Afirilu          

•            Real Madrid da Barcelona          

Spanish La Liga Asabar 27 ga watan Afirilu            

•            Sociedad da Real Madrid

Leave a comment