LA LIGA TA SANAR DA RANA DA LOKACIN WASAN SOCIEDAD DA REAL

La Liga ta sanar da rana da lokacin da za a buga wasa tsakanin Real Sociedad da Real Madrid.

A ranar Real Madrid za ta ziyarci Sociedad a wasan mako na 33 da karfe 5:00 agogon Nigeria ranar Asabar 27 ga watan Afirilu.

Kungiyoyin sun fara wasa a La Liga ranar 27 ga watan Satumbar 2023, inda Real ta yi nasarar cn 2-1 a babbar gasar tamaula ta Spain.

Ander Barrenebea ne ya fara ci wa Sociedad kwallo minti biyar da take leda, Real ta farke ta hannun Valverde bayan da suka koma daga hutu, sannan Joselu ya kara na biyu.

Kafin wasan na mako na 33, Real za ta kara da Athletic Bilbao ranar Lahadi 31 ga watan Maris a fafatawar mako na 30 a La Liga.

Daga nan Real za ta je gidan Mallorca domin buga wasan mako na 31 a La Liga ranar 13 ga watan Afirilu, sai ta karbi bakuncin Barcelona a El Clasico wasan mako na 31 ranar 21 ga watan Afirilu.

Kawo yanzu Real Madrid tana ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki takwas tsakaninta da Barcelona ta biyu.

Wasannin mako na 30

Ranar Juma’a 29 ga watan Maris

  • Cadiz da Granada

Ranar Asabar 30 ga watan Maris

  • Getafe da Sevilla
  • UD Almeria da Osasuna             
  • Valencia da Real Mallorca          
  • FC Barcelona da Las Palmas       

Ranar Lahadi 31 ga watan Maris

  • Celta Vigo da Rayo Vallecano    
  • Girona da Real Betis      
  • Deportivo Alaves da Real Sociedad        
  • Real Madrid da Athletic de Bilbao

Leave a comment