Leroy Sane: Ban san rawar da zan taka a Germany ba

Dan kwallon tawagar Germany da Bayern Munich, Leroy Sané ya ce bai san gurbin da koci, Julian Nagelsmann zai yi amfani da shi ba a Euro 2024 da zasu karbi bakunci.

Fifa ta dakatar da Sane daga buga wasa uku, bayan jan kati da aka yi masa cikin Nuwamba a karawar da Austria ta ci Germany 2-0.

Hakan ya sa bai yi wa Germany wasan sada zumunta da France ranar Juma’a da kuma Netherlands ranar Talata, sannn ba zai yi mata wanda za ta fafata da Ukraine ba ranar 3 ga watan Yuni.

Kenan zai buga Germany wasan sada zumunta da za ta kara da Grece ranar 7 ga watan Yuni, lokacin saura mako daya a fara Euro 2024.

Germany za ta fara wasan farko ranar 14 ga watan Yuni a karawa da Scotland a Euro 2024.

Sai dai Nagelsmann ya ce Sane yana cikin tsarin ‘yan wasan da zai yi amfani da si a gasar.

Leave a comment