Za a bayar da belin Alves idan ya biya £853,000

Wata kotu a Spain ta sanar cewar za a iya bayar da belin Dani Alves da zarar ya biya £853,000.

A watan jiya aka yankewa Alves hukuncin daurin shekara hudu da rabi, bayan da aka same shi da laifin fyade a gidan rawa a Barcelona a 2022.

Ranar Litinin kotun a Spain ta bayar da umarnin bayar da shi beli da zarar tsohon dan kwallon tawagae Brazil da Barcelona ya daukaka kara.

Alves mai shekara 40 na tsare a Spain tun daga Janairun 2023.

Dan wasan an tsare shi kaso daya daga cikin hukuncin da aka yanke masa kan zargin fyaden, amma ba damar ya bar kasar, zai kuma ke ziyartar kotu a kowanne mako.

Haka cikin matakan da aka ginya masa kan bayar da belin zai bayar da fasfonsa na Brazil da na Spain.

Alves ya buga wasa sama da 400 a Barcelona da lashe La Liga shida da Champions League uku, yana cikin tawagar Brazil da ta dauki kofin duniya a 2022.

Ya kuma lashe kofi a Sevilla da Juventus da kuma PSG, yana cikin ‘yan wasan Brazil da suka buga wa kasar tamaula da yawa mai wasa 126.

Leave a comment