Maguire da Walker ba za su buga wasan Belgium ba

Harry Maguire da Kyle Wwalker da mai tsaron raga, Sam Johnstone, ba za su buga wa tawagar England wasan sada zumunta da Belgium ba ranar Talata.

Tuni koci Gareth Southgate ya gayyaci golan Burnley, James Trafford da dan wasan Manchester City, Rico Lewis daga matasa ‘yan kasa da shekara 21 zuwa babbar tawagar.

Wannan shi ne karon farko da England ta gayyaci Trafford babbar tawagar, bayan da ya lashe kofin nahiyar Turai a gasar matasa ‘yan kasa da shekara 21 a bara.

Shi kuwa Lewis, mai shekara 19 ya fara yi wa Three Lions cikin watan Nuwamba a fafatawa da Arewacin Macedonia.

Kyaftin din Manchester City, Walker ya ji rauni a wasan sada zumunta da Brazil ta ci England 1-0 ranar Aasabar a Wembley.

Tuni dai Maguire da Walker da dan kwallon Crystal Palace, Johnstone, suka koma kungiyoyinsu don ci gaba da jinya.

Tuni aka sanar da cewar mai taka leda a Bayern Munich, Harry Kane na dauke da rauni da shi da Bukayo Saka, wadanda ba su buga fafatawar ta ranar Asabar ba.

Leave a comment