Man United za ta ke bai wa McTominay £120,000 duk mako

Manchester United za ta bai wa Scott McTominay sabuwar yarjejeniyar da za ta kai £120,000 a kowanne mako.

Dan kasar Scotland, an yi ta alakanta shi da zai bar Old Trafford tun kan fara kakar bana da cewar West Ham United zai koma da taka leda.

An ce Fulham ma ta yi kokarin sayen McTominay a lokacin da Bayern Munich ta so daukar Joao Palhinha cikin da bai samu yi wu ba.

Sai dai mai shekara 27 shi ne kashin bayan United karkashin Erik Ten Hag a kakar 2023-24 da buga wasa 34a dukkan fafatawa da cin kwallo tara da bayar da uku aka zura a raga.

Kamar yadda Daily Star ta wallafa ta ce United ta yanke shwarar gina kungiyar karkashin McTominay, wadda ta tsara masa kunshin kwantiragi mai tsoka da zai amince nan take.

Tuni ake cewa Sir Jim Ratcliffe ya amince a shirya yarjejeniyar da za a ke bai wa dan kwallon £120,000-a-kowanne mako, kenan zai ninka albashin da yake karba.

McTominay yana da kunshin kwantiragi a Old Trafford da zai kare a karshen Yunin 2025 da cewar za a iya tsawaita masa kaka daya da zarar ya taka rawar gani.

Yaci kwallo bakwai ya bayar da daya aka zura a raga a karawa 25 a Premier League a kakar nan, ya kuma ci Liverpool a FA Cup da United ta yi nasarar 4-3 zagayen daf da na kusa da na karshe.

McTominay yana tare da United tun yana matashin dan shekara biyar, wanda ya dunga taka mataki daga na reno har zuwa babbar kungiyar wadda ya fara yi wa tamaula a karon farko a 2017.

Dan kasara Scotnald ya buga wasa 243 a Red Devils dacin kwallo 28 da bayar da takwas aka zura a raga a dukkan fafatawa.

Haka kuma McTominay yana daga kashin bayan tawagar Scotalnd, wadda ya buga wa wasa 48 tun bayan da ya fara taka mata leda a 2018 da cin kwallo takwas da bayar da uku aka zura a raga.

Leave a comment