Real madrid za ta kara wa Kross shekara daya

Wasu rahotanni na cewar Real Madrid za ta kara wa Toni Kross kwantiragin kaka daya.

Mai shekara 34 yana daga cikin kashin bayan kungiyar a kakar nan, wanda ya yi mata wasa 38 a dukkan fafatawa da cin kwallo daya da bayar da bakwai aka zura a raga.

Tun farko yarjejeniyar Kross za ta karkare a karshen watan Yunin bana, amma Real Madrid na shirin tsawaita masa shekara daya.

Kross ya koma buga wa tawagar Jamus tamaula ranar Asabar a karawar sada zumunta da France, shi ne ya bara da kwallon da Florian Wirtz ya zura a raga a wasan.

Tun farko dan wasan ya yi ritaya bayan kammala Euro 2020, amma yanzu ya sake komawa yi wa kasar tamaula mai shirin karbar bakuncin Euro 2024 a cikin watan Yuni.

Kross ya koma Real Madrid daga Bayern Munich a 2014, wanda ya yi kungiyar Spain wasa 455 da cin kwallo 28 da bayar da 96 aka zura a raga kawo yanzu.

Tuni dan wasan ya lashe La Liga uku da Copa del Rey daya da Spanish Super Cup hudu da Champions League hudu da UEFA Super Cup uku da Club World Cup biyar.

Shima Luka Modric kwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan, amma dan kasar Croatia ya rasa gurbinsa a Real Madrid a kakar nan, kenan zai nemi wata kungiyar bayan kammala kakar nan.

Leave a comment