Tottenham ta kammala daukar aron Timo Werner

Dan kwallon tawagar Germany, Timo Werner zai je  buga wasannin aro a Tottenham daga RB Leipzig.

Mai shekara 27, zai je London domin auna koshin lafiyarsa, kuma Tottenham ce za take biyan albashinsa zuwa karshen kakar nan.

Werner na fatan Tottenham za ta yi amfani da shi sosai, domin ya samu wakiltar Germany a Euro 2024.

Tottenham za ta ci gaba da wasannin ba tare da kyaftin, Son Heung-min ba, wanda zai wakilci South Korea a Asian Cup da za a yi a Qatar a cikin watan nan na Janairu.

Werner, mai shekara 27 ya taka leda a Premier League a Chelsea tsakanin 2020 zuwa 2022.

Ya koma Leipzig kaka biyu da ta wuce daga kungiyar Stamford Bridge, wadda a baya ya buga mata tamaula tsakanin 2016 zuwa 2020.

Yanzu haka Werner yana Spain tare da Leipzig a La Manga inda kungiyar ke atisaye, bayan hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Werner ya buga wa Germany wasa 57, wadda rabon da ya buga mata tamaula tun wasan sada zumunta da Belgium a cikin Maris din 2023.

Leave a comment