Arteta ya bukaci Arsenal su doke Liverpool ba sai sun yi wasa biyu ba a FA Cup

Mikel Arteta ya nemi Arsenal ta yi kokari ta lashe wasan FA Cup da Liverpool ranar Lahadi ba tare da kara fuskantar kungiyar a karo na biyu ba a gasar.

Arteta ya ce rashin cin wasan farko zai kara sa kungiyar cikin matsi a buga wasa daf-da-daf da suke gabanta.

Arsenal mai maki 40 a mataki na hudu a teburin Premier League za ta karbi bakuncin Liverpool ta daya mai maki 45.

Idan Arsenal ta buga wasa da Liverpool ranar Lahadi za ta yi hutun kwana 13, amma idan ta tashi canjaras za ta kara fuskantar wasa na biyu a FA cup a wani makon.

Sannan za ta buga Premier League ranar 20 ga watan Janairu da Crystal Palace a karawar hamayya.

Arteta ya ce dan hutun da yake tsakani ba yawa, saboda haka ya kamata Gunners ta doke Liverpool ranar Lahadi.

Arsenal za ta fafata a wasa hudu tsakani a Premier League kafin ta fuskanci Porto a Champions League ranar 21 ga watan Fabrairun 2024.

Wasannin da za a buga a zagaye na uku a FA Cup ranar Lahadi:

  • Manchester City da Huddesfield Town
  • Luton Town da Bolton Wanderers
  • West Ham United da Bristol City
  • Peterborough United da Leeds United
  • Shrewsbury Town da Wrexham
  • West Brom da Aldershot Town
  • Nottingham Forest da Blackpool
  • Arsenal da Liverpool

Leave a comment