Kim Minjae ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon South Korea

Mai tsaron bayan, Bayern Munich, Kim Minjae ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon South Korea, kamar yadda hukumar kwallon kafar ta sanar.

Mai shekara 27, ya taimakawa Napoli ta lashe Serie A na bara a karon farko bayan shekara 33.

Kuma shi ne aka bayyana a matakin fitatcen mai tsaron baya a babbar gasar tamaula ta Italy a kakar da ta wuce.

Daga nan ne ya koma Bayern Munich a cikin watan Agusta kan €50, wanda kawo yanzu ya buga wasa 22 da cin kwallo daya a kungiyar da ke rike da Bundesliga.

Kim zai wakilci South Korea a Asian Cup da za a yi a Qatar daga 12 ga watan Janairu.

South Korea mai Asian Cup biyu tana rukunin da ya hada da Malaysia da Jordan da kuma Bahrain.

Kenan Kim ba zai buga wasa shida ba a Bundesliga idan ya je Asian Cup, har da karawar hamayya ranar 10 ga watan Fabrairu da Bayern Leverkusen.

Leave a comment