Liverpool ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin Premier League

Liverpool ta yi zamanta a kan teburin Premier League, bayan da ta doke Newcastle United 4-2 ranar Litinin a Anfield.

Mohamed Salah ya ci kwallo biyu a karawar da ta bai wa Liverpool damar bai wa Aston Villa ta biyu tazarar maki uku, bayan karawar mako na 20.

Tun farko Salah, wanda zai je Masar domin zuwa gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a Janairun nan ya barar da bugun fenariti.

Kwallon farko da Salah ya zura a ragar Newcastle United shi ne na 150 a Premier League daga baya Alexander Isak ya farke.

Sai kuma Curtis Jones ya ci wa Liverpool na biyu da kuma Cody Gapko ya kara na uku a raga.

Newcastle ta zare daya ta hannun Sven Botman, wasa ya koma 3-2, sai Salah ya ci na hudu na kuma biyu a karawar.

Liverpool ta ci wasa bakwai a gida da fara Premier League ta bana, amma kungiyar ta kasa nasara a kan Manchester United da Arsenal a karawa biyu da ta yi a Anfield.

Da wannan sakamakon Liverpool ta bai wa Aston Villa ta biyu tazarar maki uku da tazarar maki biyar tsakani da Manchester City, mai kwantan wasa – Arsenal ce ta hudu da maki 40 iri daya da na Man City.

Newcastle, wadda ta buga wasan ba tare da fitattun ‘yan kwallonta tara ba, sakamakon jinya tana ta taran teburin Premier League.

Leave a comment