Soucek zai ci gaba da taka leda a West Ham zuwa 2027

Tomas Soucek ya amince da kunshin yarjejeniyar ci gaba da taka leda a West Ham United zuwa karshen watan Yunin 2027.

Dan wasan jamhuriyar Czech, mai shekara 28 ya ci kwallo 30 a wasa 182, tun bayan da ya koma kungiyar daga Slavia Prague a Janairun 2020, wanda ya nuna kansa bayan fara wasannin aro.

Tun farko kwantiragin dan kwallon zai kare a karshen kakar bana, yanzu zai ci gaba da taka leda a kungiyar London mai buga Premier League zuwa 2027.

West Ham ta lashe Europa Conference League a kakar da ta wuce  – kofinta na farko a shekara 43, wadda yanzu take ta shida a teburin Premier League a bana.

Leave a comment