Asian Cup 2024: An gayyaci Mitoma tawagar Japan

Kociyan tawagar kwallon kafar Japan, Hajime Moriyasu ya gayyaci dan wasan Brighton, Kaoru Mitoma cikin jerin ‘yan wasan da za su buga wa kasar Asian Cup a bana.

Mai horar da Brighton, Roberto de Zerbi ya sanar a makon jiya cewar Mitoma zai yi jinyar mako shida, bayan raunin da ya ji a gasar Premier da Crystal Palace ranar 21 ga watan Disamba.

Duk da haka Japan ta gayyaci dan wasan cikin mutum 26 a gasar ta Asian Cup da za a yi a Qatar daga 12 ga watan Janairu.

Japan ta dauki Asian Cup guda hudu jimilla, amma an doke ta 3-1 a wasan karshe a Qatar a 2019 a karawar da suka yi a Hadaddiyar Daulal Larabawa.

‘Yan wasa 14 aka gayyata daga cikin wadanda suka buga wa Japan kofin duniya a 2022 a Qatar, wadanda suka doke Germany da Spain daga baya ta yi rashin nasara a hannun Croatia a zagayen ‘yan 16.

Japan tana rukuni na hudu a gasar Asian Cup da ya hada da Indonesia da Iraq da kuma Vietnam.

Tawagar Japan:

Masu tasron raga: Daiya Maekawa (Vissel Kobe), Zion Suzuki (Sint-Truiden/BEL), Taishi Brandon Nozawa (FC Tokyo)

Masu tsaron baya: Shogo Taniguchi (Al-Rayyan/QAT), Kou Itakura (Monchengladbach/GER), Tsuyoshi Watanabe (Gent/BEL), Yuta Nakayama (Huddersfield/ENG), Koki Machida (Union SG/BEL), Seiya Maikuma (Cerezo Osaka), Takehiro Tomiyasu (Arsenal/ENG), Hiroki Ito (Stuttgart/GER), Yukinari Sugawara (AZ/NED)

Masu buga tsakiya da masu cin kwallo: Wataru Endo (Liverpool/ENG), Junya Ito (Reims/FRA), Takuma Asano (Bochum/GER), Takumi Minamino (Monaco/FRA), Hidemasa Morita (Sporting/POR), Kaoru Mitoma (Brighton/ENG), Daizen Maeda (Celtic/SCO), Reo Hatate (Celtic/SCO), Ritsu Doan (Freiburg/GER), Ayase Ueda (Feyenoord/NED), Keito Nakamura (Reims/FRA), Kaishu Sano (Kashima Antlers), Takefusa Kubo (Real Sociedad/ESP), Mao Hosoya (Kashiwa Reysol)

Leave a comment