Bayanai kan wasan Liverpool da Newcastle

Liverpool ta karbi bakuncin Newcastle, domin buga Premier League ranar Litinin a Anfield.

Liverpool mai maki 42 tana ta daya a teburin Premier League, ita kuwa Newcastle mai maki 39 tana ta tara a teburin.

Sun kara a bana ranar 27 ga watan Agustan 2023, inda Liverpool ta ci 2-1 a St James Park.

Watakila Alexis Mac Allister ya yi zaman benci, bayan da bai buga karawa shida ba, sakamakon raunin da ya yi.

‘Yan wasan Liverpool da ke jinya sun hada da Andy Robertson da Kostas Tsimikas da Joel Matip da Ben Doak da Thiago Alcantara da kuma Stefan Bajcetic.

Kimanin ‘yan kwallon Newcastle tara ne ke jinya, koda yake Jamaal Lascelles, rauninsa bai yi muni ba.

Joelinton ya koma buga wa Newcastle tamaula ranar 1 ga Kirsimeti, bayan da ya sha jinya.

Wasa tsakanin Liverpool da Newcastle:

Wasa 14 Liverpool ta buga da Newcastle ba a doke ta ba a bayan nan, tun bayan 2-0 da ta yi rashin nasara a St James Park a Disambar 2013, wata biyu tsakani da Jurgen Klopp ya fara aiki.

Newcastle ta kasa yin nasara daga wasa 27 da ta ziyarci Liverpool a dukkan fafatawa da canjaras biyar da rashin nasara 22 daga ciki.

Wasa na karshe da Newcastle ta doke Liverpool a Anfield tun a Nuwambar 1995 a League Cup.

A karawar Premier kuwa ta karshe da Newcastle ta yi nasara a Anfield tun Afirilun 1994.

Wasa uku baya da suka kara a ranar shiga sabuwar shekara, Newcastle ce ta yi nasara biyu a gida da canjaras daya.

Leave a comment