Nottingham Forest za ta karbi bakuncin Manchester United

Nottingham Forest za ta karbi bakuncin Manchester United a wasan Premier League ranar Asabar a City Ground.

Man United tana mataki na bakwai a kan teburin Premier League da maki 31, Forest mai maki 17 tana ta 16.

To sai dai dan wasan Forest, Ibrahim Sangare ba zai yi karawar ba, wanda aka bai wa katin gargadi biyar, amma Willy Boly ya kammala hukuncin dakatarwa.

Har yanzu Serge Aurier da Felipe da kuma Taiwo Awoniyi na jinya, amma Nuno Espirito Santo bai da sabbin ‘yan wasan da suka ji rauni.

Watakila Manchester United ta yi wasan ba tare da Luke Shaw da Sofyan Amrabat da kuma Anthony Martial.

Masu jinya a kungiyar sun hada da Casemiro da Harry Maguire da Tyrell Malacia da Lisandro Martinez da Mason Mount da kuma Victor Lindelof.

Abinda ya kamata ku sani kan wasan:

Wannan shi ne karo na 101 da za a fafata tsakanin Forest da Manchester United.

Forest ta yi nasara a 33 da canjaras 24, yayin da Manchester United ta ci wasa 53.

Kungiyoyin sun kara a bana a Premier League ranar 26 ga watan Agustan 2023, inda Man United ta yi nasara da cin 3-2.

Manchester United ta lashe wasa 11 a jerehave a karawada Forest a dukkan fafatawa, tun bayan 1-1- da suka tashi a Premier League ranar 27 ga watan Nuwambar 1995 a City Ground.

won 11 consecutive matches against Nottingham Forest in all competitions since drawing 1-1 at the City Ground in the Premier League on 27 November 1995.

Wasa da Forest ta ci Man United a Premier League a karawa 13 baya, shi ne 2-1 a Old Trafford a cikin Disambar 1994.

Wasa na baya-baya da Forest ta yi nasara a kan Man United a       gida shi ne a karawar rukunin farko a Maris din 1992 da cin 1-0.

Leave a comment