Barcelona ta dauki Vitor Rogue

Barcelona ta sanar da daukar Vitor Roque kan yarjejeniyar da za ta kare a kungiyar Camp Nou zuwa karshen Yunin 2031.

Tun farko an tsara Rogue zai koma Camp Nou a karshen kakar 2024, amma yanzu zai iya buga mata tamaula da za ta fafata da Las Palmas ranar 4 ga watan Janairu.

Wasu rahotanni na cewar Barcelona ta gindaya 434.7miliyon ga duk mai son daukar kwallon Brazil idan kwantiragin bai kare ba.

A bara ne Roque ya koma Athletico Paranaense, wadda kawo yanzu ya ci mata kwallo 28 a wasa 81, ya bayar da 11 aka zura a raga.

Mai shekara 18 ya fara buga wa babbar tawagar Brazil wasa cikin watan Maris a wasan sada zumunta da Morocco ta ci 2-1.

Sai dai dan kwallon ya ji raunin da ya hana shi buga wa Brazil wasan neman shiga gasar kofin duniya da ta yi da cikin Oktoba da Nuwamba.

Tuni Barcelona ta ce matashin zai fara atisaye ranar Juma’a da zarar ‘yan wasa sun koma karbar horo, bayan bikin Kirsimeti.

Barcelona ta doke Almeria 3-2 ranar 20 ga watan Disamba daga nan aka yi hutun Kirsimeti, wadda take mataki na hudu a teburin LaLiga da maki 38

Idan har Barcelona ba ta yi amfani ba da Roque ba a karawa da Las Palmas ranar 4 ga watan Janairu.

Kenan za a sa rai zai kara a Copa del Rey da Barbastro ranar 7 ga watan Janairu.

Leave a comment