Son Heung-min zai ja ragamar South Korea zuwa Asian Cup

Ranar Alhamis, kociyan South Korea, Jurgen Klinsman ya bayyana dan wasan Tottenham, Son Heung-min a matakin wanda zai ja ragamar tawagar zuwa Asian Cup na bana.

Rabonda kasar ta lashe babban kofin nahiyar tun bayan shekara 64.

Dan wasan Wolves, Hwang Hee-chan, wanda ya ci kwallo na 10 a Premier League a bana a wasa da Brentford ranar Laraba, yana cikin ‘yan wasa 26 da Klinsmann ya sanar, domin buga wasannin da za a fara a Qatar daga ranar 12 ga watan Janairun 2024.

Son ne kyaftin din tawagar da ta hada da dan wasan da ke taka leda a Bayern Munich, Kim Min-jae da matashi mai shekara 22 da ke wasa a Paris Saint-Germain, Lee Kang-in.

Rabonda South Korea ta dauki Asian Cup tun bayan 1960.

An hada South Korea a rukuni na biyar da ya hada da Malaysia da Jordan da kuma Bahrain.

Son zai buga Asia Cup na hudu jimilla, yana cikin ‘yan wasan South Korea da suka yi rashin nasara a karawar karshe a hannun Australia a 2015.

Leave a comment