Peru ta nada Jose Fossati sabon kociyanta

Hukumar kwallon kafa ta Peru ta sanar da nada dan kasar Uruguay, Jorge Fossati a matakin sabon kociyanta.

Hukumar ta ce ta dauki kocin saboda kwarewar da yake da ita, domin ya kai kasar gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Mexico da kuma Canada.

Fossati ya taba jan ragamar kungiyar Peru da ke Lima, Club Universitario de Deportes ta lashe babban kofin gasar kasar da ake kira Liga 1.

Haka kuma ya horar da tawagar Uruguay da kuma ta Qatar.

Har yanzu Peru ba ta ci wasa ba a karawar da take a neman shiga gasar kofin duniya, wadda ta hada maki biyu daga wasa shida.

Ita ce ta karshe a teburin Kudancin Amurka da tazarar maki uku tsakaninta da Paraguay a matakin zuwa wasannin cike gurbi, bayan da biyar din farko ke wakiltar nahiyar kai tsaye.

Kawo yanzu Argentina ce ta daya a kan teburin Kudancin Amurka da maki 15, sai Uruguay biye da ita da maki 13.

Peru ba ta samu zuwa gasar kofin duniya a Qatar ba a 2022, wadda aka fitar da ita a karawar cikin rukuni a babbar gasar tamaula ta duniya da aka yi a Rasha a 2018.

Gasar farko da Peru ta halarta kenan tun bayan 1982.

Leave a comment