A watan Janairu Haaland zai koma wasa – Guardiola

Pep Guardiola ya sanar cewar a cikin watan Janairu Erling Haaland zai koma buga wa Manchester City wasanni.

Kenan ba zai yi wa kungiyar wasan karshe a 2023 ba da za ta kara da Sheffield United ranar Asabar 30 ga watan Disamba.

Rabon da dan kwallon tawagar Norway ya buga wa Man City wasa tun bayan da Aston Villa ta yi nasarar cin 1-0 a farkon watan nan.

Jimilla Haaland wanda ke jinyar rauni a kafa bai yi wa Man City wasa shida ba, har da biyu a kofin duniya na zakarun nahiyoyi da aka yi a Saudi Arabia, wanda Man City ta lashe.

Duk da bai yi mata wasannin ba, Man City ta doke Urawa Red Diamonds ta Japan da ta Brazil, Fluminense, sannan ta dauki kofin a karon farko a tarihi.

Kenan Man City ta zama ta farko a England ta dauki kofi biyar a cikin shekara daya, da ya hada da Champions League da Uefa Super Cup da Fifa World Club Cup da Premier League da kuma FA Cup.

Haka kuma Haaland bai buga wasan da Manchester City ta doke Everton 3-1 ranar Laraba a Premier League a Goodison Park.

Yanzu abinda ya rage shi ne a wane wasan ne Haaland zai koma buga wa Man City tamaula a Janairun 2024?

Man City za ta fara wasa a sabuwar shekara a FA Cup da za ta fuskanci Huddersfield Town ranar 7 ga watan Janairu, sannan ta ziyarci St James Park domin karawa da Newcastle United a Premier League.

Duk da Haaland na jinya shi ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Premier League mai 14 a raga a wasa 15 a bana.

Leave a comment