Bayanai kan wasan Arsenal da West Ham a Premier League

Arsenal za ta kara da West Ham United a wasan hamayya a karawar mako na 19 a Premier League ranar Alhamis.

Arsenal tana mataki na biyu da maki 40 a teburin Premier League da Liverpool ke jan ragama da tazarar maki biyu.

West Ham United kuwa mai maki 30 tana ta bakwai a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.

Karawa tsakanin kungiyoyin biyu:

Arsenal ta ci wasa 12 daga 13 baya da ta kara da West Ham a lik, dayan da aka doke ta shi ne 2-0 a kakar 2015-16.

West Ham ta yi rashin nasara 35 a Premier League da take fuskantar Arsenal – karawar da ake doke ta da yawa kenan tare da wanda take fuskantar Liverpool.

Arsenal

Duk kungiyoyin da ke jan ragamar teburin Premier League kwana daya da Kirsimeti wato 26 ga watan Disamba, sun lashe kofi 10 daga kaka 14 baya da aka buga.

Sai dai Gunners ta kasa daukar kofin daga kaka shida baya da take zama ta daya a ranar 25 ga watan Disamba.

Ba a yi nasara ba a wasa 17 a Premier League da Arsenal take fuskantar kungiyoyin Landan, tun bayan doke ta 3-0 da Tottenham ta yi a Mayun 2022, wadda ta yi nasara 12 da canjaras biyar daga ciki.

Mikel Arteta bai yi rashin nasara ba a wasa 13 da Arsenal ta buga a gida a lik da kofi ba, wanda ya ci wasa 11 da canjaras biyu, wanda bakwai daga ciki da ya yi nasara ya ci kwallo 21-2.

West Ham United

Idan West Ham ta yi nasara za ta hada maki 33 tun kan buga zagaye na biyu a Premier League – kwazo mai kyau da za ta yi kenan a tarihi.

Ta yi nasarar lashe wasa biyar daga bakwai da ta fafata a bayan nan, wasan da Fulham ta doke 5-0 ne ta yi rashin nasara daga ciki.

West Ham na bukatar cin kwallo daya ta cika 300 da za ta zura a raga a wasan hamayya a Premier League da kungiyoyin Landan.

David Moyed na turba rashin nasara ta 239 a Premier League, ba kocin da ya kai shi wannan tarihin mara dadin ji.

Moyes bai ci wa sa ba a fafatawa 72 a Premier League a maatakinsa na koci da ya kai ziyara Arsenal da Chelsea da Liverpool da kuma Manchester United (Yayi canjaras 21, da rashin nasara 51).

Leave a comment