Hojlund ya kawo karshen kamfar cin kwallo a Premier League

Manchester United ta doke Aston Villa 3-2 a wasan mako na 19 a Premier League ranar Talata a Old Trafford.

Tun farko Villa ta zura kwallo biyu a raga, haka suka je hutu, an ci Man United.

John McGinn da Leander Dendoncker suka ciwa Villa kwallayen daga baya Man United ta kara sa kaimi.

Sai Alejandro Garnacho ya farke ta farko da kuma ta biyu daga baya Rasmus Hojlund ya ci na ukun.

Kenan kwallon farko da Hojlund ya ci wa Man United a Premier League a dukkan karawar da ya yi mata.

Kuma kwallon farko da ya ci a gasar Ingila amma na shida da ya zura a raga a wasa 15 da ya yiwa Man United.

Dan wasan, wanda ya koma Old Trafford da taka leda daga Atalanta a cikin watan Agusta ya ci wa Man United kwallo biyar a Champions League.

Koda yake Man United ta yi ta karse a rukunin farko da hakan ta kasa kai wa zagaye na biyu ko buga gurbin shiga Europa League.


Nasarar da Man United ta samu ta kawo karshen wasa hudu ba tare da nasara ba a dukkan fafatawa, kuma hakan ya sa ta koma ta shida a teburin Premier League.


Ita kuwa Villa ta yi wasa biyu daga ciki ta yi canjaras daya da wanda Man United ta doke ta ranar Talata.

Kungiyar ta Unai Emery ta ci gaba da zama ta ukun teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Liverpool ta daya.

Kawo yanzu Man United ta yi rashin nasara wasa 13 a dukkan fafatawa a bana, kaka mafi muni da take buga wa tun bayan 1930.

Duk da haka Erik ten Hag na ta kokarin nunawa Sir Jim Ratcliffe cewar zai iya mayar da kungiyar kan ganiya.

A makon nan Ratcliffe ya mallaki hannu jarin Man United kaso 25 cikin 100 da ya kai kimanin £1.03 billion.

Leave a comment