Bayanai kan wasan Burnley da Liverpool a Premier League

Liverpool ta ziyarci Burnley domin buga wasa na 19 a Premier League ranar Talata a Turf Moor.

Liverpool tana ta 19 a teburin Premier da maki 39 da tazarar maki daya tsakaninta da Arsenal ta daya.

Ita kuwa Burnley tana mataki na 19 ta biyun karshen teburi mai maki 11, bayan karawa 18.

Watakila ‘yan wasan Burnley, Johann Berg Gudmundsson da Jack Cork da kuma Aaron Ramsey su buga wasan bayan jinya.

Har yanzu Luca Koleosho na jinya, bayan raunin gwiwar kafa.

Dan wasan Liverpool, Kostas Tsimikas zai yi jinya, bayan raunin da ya ji a karawar da Liverpool da Arsenal suka raba maki ranar Asabar.

Haka koci, Jurgen Klopp bai da tabbaci ko Luis Diaz zai iya buga wasan.

Har yanzu a Liverpool Alexis Mac Allister da Diogo Jota da kuma Andrew Robertson na jinya.

Batutuwa kan karawar kungiyoyin

Liverpool ta ci wasa bakwai daga takwas a Premier League da Burnley a Turf Moor.

Wasa biyu Burnley ta yi nasara a kan Liverpool daga 16 baya a Premier League, shi ne a gida cikin Agustan 2016 da a Anfield a Janairun 2021.

Burnley

Burnley ta yi rashin nasara takwas daga wasa tara a gida a Premier League a kakar nan.

Ta hada maki biyar a wasan waje fiye da wanda ta samu a gida a bana.

Ta yi rashin nasara biyar daga wasa bakwai baya ranar 26 ga watan Disamba – wanda ta ci shi ne doke Middlesbrough a 2016.

Liverpool

Liverpool ta zura kwallo a wasa 13 da ta buga a waje da cin 30 a cikin fafatawar.

Kungiyar Anfield ta amfana da maki 19 daga wasan da ake fara cinta daga baya ko dai ta farke ko kuma ta lashe karawar.

Liverpool ta cinye dukkan wasa shida ranar 1 da kammala Kirsimeti, tun bayan rashin nasara a hannun Manchester City 2-1 a 2013.

Mohamed Salah yana da hannu kai tsaye a cin kwallo 13 a karawar Liverpool 13 a waje, wanda ya ci biyar ya bayar da 10 aka zura a raga.

Leave a comment