Man United ta yi shekara 45 ba a doke ta ba a Premier League ranar 1 ga Kirsimeti

Ranar Talata Manchester United za ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan mako na 19 a gasar Premier League.

Wasan za ta buga ne kwana daya da yin bikin Kirsimeti, wato 26 ga watan Disamba, wadda ta yi shekara 45 ba a doke ta ba a irin wannan ranar.

Wasannin da suka buga a bara 2022/2023

Premier League Asabar 30 ga watan Afirilu 2023

  • Man United     1 – 0 Aston Villa       

EFL CUP Alhamis 10 ga wata Nuwambar 2022        

  • Man United     4 – 2 Aston Villa       

Premier League Lahadi 6 ga watan Nuwambar 2022        

  • Aston Villa        3 – 1 Man United

A karshen mako Manchester United ta tabbatar da cewar Sir Jim Ratcliff ya mallaki kaso 25 cikin 100 na kungiyar Old Trafford, amma ana jiran Premier League ta amince.

Man United ta buga karawa 19 a Old Trafford ranar 1 da kammala Kirsimeti, wadda ta ci fafatawa 16 da canjaras uku.

Haka kuma ba wata kungiya a Ingila da ta ci wasa da yawa ranar ta 26 ga watan Disamba a Premier League, fiye da Man United mai 53.

To sai dai Man United ta yi wasa uku a lik ba tare da yin nasara ba ko zura kwallo a raga a bana, hakan ya sa kungiyar ta yi kasa zuwa mataki na takwas a teburi.

Haka kuma Man United na gudun kada a doke ta karo uku a jere a Old Trafford a karon farko tun 1962 karkashin Sir Matt Busby.

Man United ta taba yin wasa hudu ba tare da cin kwallo ba a raga a 1992, wadda ba ta fatan hakan ya faru da ita ranar Talata.

Tuni dai Erik ten Hag ya yi rashin nasara 13 a dukkan fafatawa a bana, kwazo mafi muni a kungiyar tun bayan 1930.

Leave a comment