Bundesliga 2023/24: Za a koma wasanni cikin Janairu

Babbar gasar tamaula ta Jamus, wato Bundesliga na hutu, bayan da aka kammala karawar mako na 16.

Hakan zai bai wa kungiyoyi da ‘yan wasa da ‘yan kallo damar yin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

An kammala wasannin mako na 16 ranar Laraba 20 ga watan Disamba,kenan an ci rabin kakar bana.

An fara kakar Bundesliga ta bana ranar 18 ga watan Agustan 2023, wadda kawo yanzu an yi wasa 143, an ci kwallo 480.

Haka kuma dan wasan Bayern Munich, Harry Kane, wanda ya koma kungiyar kan fara kakar bana daga Tottenham yana da 21 a raga.

Wasan da aka ci kwallaye a gida da yawa shi ne wanda Bayern Munich ta dura 8-0 a ragar Darmstadt.

Haka kuma karawar da aka ci kwallaye da yawa a waje shi ne wanda Bayern Munich ta je ta durawa Bremen 4-0.

Wasannin da aka ci kwallaye da yawa shi ne wanda aka tashi 4-4 tsakanin Augsburg da Munchengladbach da wanda Bayern Munich ta dura 8-0 a ragar Darmstadt.

Bayern Leverkusen ta yi wasa takwas a jere ba tare da an doke ta ba, wadda jimilla ta yi karawa 16 ba tare da rashin nasara ba.

Kungiyar Berlin ce ta yi fafatawa 10 ba tare da yin nasara ba, wadda aka doke ta tara daga ciki.

Wasa takwas a Bundesliga ya karbi ‘yan kallo da yawa, yayin da guda bakwai aka samu karancin ‘yan kallo.

Bayern Leverkusen ce ta daya a Bundesliga mai maki 42, sai Bayern Munich mai kwantan wasa da maki 38.

Stuttgard mai maki 34 tana ta uku da RB Leipzig mai maki 33 da kuma Borussia Dortmund ta biyar da maki 27

Wwadanda ke ukun karshen teburin Bundesliga sun hada da Mainz ta 16 da Koln daDamstadt ta 18 da kowacce take da maki 18.

Jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye:

  1. Harry Kane Bayern Munich 21
  2. Serhou Guirassy Stuttgart 17
  3. Lois Openda RB Leipzig 11
  4. Victor Boniface Bayer Leverkusen 10
  5. Jonas Wind Wolfsburg 9
  6. Deniz Undav Stuttgart 9
  7. Leroy Sane Bayern Munich 8
  8. Ermedin Demirovic Augsburg 8

Wasannin mako na 17 a Bundesliga

Ranar Asabar 13 ga watan Janairu

  • Freiburg da Union Berlin
  • FC Koln da Heidenheim 1846 
  • FSV Mainz 05 da VfL Wolfsburg     
  • Augsburg da Bayer 04 Leverkusen
  • RB Leipzig da Eintracht Frankfurt  
  • Darmstadt 98 da Borussia Dortmund    

Ranar Lahadi 14 ga watan Janairu

  • VFL Bochum da Werder Bremen   
  • Borussia Monchengladbach da VfB Stuttgart 

Leave a comment