Karo na biyu a jere Arsenal tana ta daya a Premier kan Kirsimeti

Kungiyar Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League, bayan kammala wasa 18 a kakar bana.

Hakam na nufin Gunners ce ke kan gaba tun kafin Kirsimeti karo na biyu kenan a jere.

Kawo yanzu Gunners ta ci wasa 12 da canjaras hudu aka doke ta fafatawa biyu.

Ta hada maki 40 daga wasa 18 da cin kwallo 36 aka zura mata 16 a raga kawo yanzu.

A kakar bara bayan karawar mako na 18, Arsenal ce ta daya a kan teburi da maki 46, bayan cin wasa 15 da canjaras daya aka doke ta sau biyu kacal.

Manchester City ce ta biyu a kakar da maki 42, bayan ci karawa 13 da canjaras uku da rashin nasara biyu.

Daga baya kungiyar Etihad ta karbe matakin ta kuma lashe Premier League, wadda ta hada da FA Cup da kuma Champions League.

A kakar da ta wuce Arsenal ta yi kwana 248 a kan matakin farko a teburin Premier amma ba ta dauki kofin ba.

Arsenal, wadda ba ta taba daukar Champions League na fatan daukar Premier League a bana, rabonta da shit n shekara 20.

Wasannin mako na 19 da za a buga a Premier League:

Ranar Talata 26 ga watan Disamba

  • Newcastle United da Nottingham Forest        
  • Bournemouth da Fulham
  • Sheffield United da Luton Town             
  • Burnley da Liverpool
  • Manchester United da Aston Villa 

Ranar Laraba 27 ga watan Disamba          

  • Brentford da Wolverhampton Wanderers        
  • Chelsea da Crystal Palace       
  • Everton da Manchester City  

Ranar Alhamis 28 ga watan Disamba     

  • Brighton da Tottenham
  • Arsenal da West Ham United

Leave a comment