Sir Ratcliff ya sayi kaso 25 cikin 100 na Manchester United

Shugaban INEOS, Sir Jim Ratcliff ya amince da sayen kaso 25 cikin 100 na Manchester United.

Kenan kudin ya kai £1.25 billion, zai karbi ragamar gudanar da kungiyar da ke Old Trafford kenan.

Manchester United mai buga gasar Premier League ce ta sanar da hakan ranar Lahadi.

Attajiri dan kasar Burtaniya, mai shekara 71 zai kuma samar da $300 million don kara bunkasa kungiyar nan gaba.

Kamar yadda kungiyar ta sanar ‘’Manchester United na sanar da kulla yarjejeniya da shugaban INEOS, Sir Jim Ratcliff zai mallaki kaso 25 cikin 100 na Manchester United, zai kuma samar da $300 million nan gaba don bunkasa kungiyar da ke Old Trafford.

‘’Cikin kunshin yarjejeniyar, INEOS ya amince da bukatar da mahukuntan kungiyar suka mika masa na daukar alhalin gudanar da kungiyar.’’

Ratciff ya sanar cewar yana son ya mayar da Man United gurbin da take kai a baya a fannin kwallon kafa a Turai da duniya.

Man United tana mataki na takwas da maki 28, bayan cin wasa tara da canjaras daya aka doke ta karo takwas, bayan wasa 18 a Premier League.

Leave a comment