Manchester United na buga kaka mafi muni tun 1930

Manchester United ta yi rashin nasara ta 13 a dukkan karawa a bana, bayan da West Ham ta doke ta 2-0 a Premier League ranar Asabar.

Karon farko da take buga kaka da rashin kokari tun bayan 1930/31 da aka doke ta 16 a irin wannan lokacin kafin Kirsimeti.

Haka kuma karon farko Man United ta yi wasa hudu a jere ba tare da ta zura kwallo ba a raga tun bayan Sir Alex Ferguson a Nuwambar 1992.

Man United, wadda take ta takwas din teburi da maki 28 ta je West Ham da kwarin gwiwa, bayan da ta tashi 0-0 da Liverpool a Anfield a mako na 17.

West United kuwa ta karbi bakuncin Man United, bayan da Liverpool ta fitar da ita a Carabao Cup da cin 5-1 a makon jiya.

Man United ta saka Marcus Rashford da Facundo Pellistri da Sergio Reguilon da Christian Eriksen, sannan ta cire Rasmus Hojlund, wanda har yanzu bai ci kwallo ba a wasannin England.

Kamar dai Erik ten Hag baya fuskantar matsi, wanda zai karbi bakuncin Aston Villa ranar Talata 26 ga watan Disamba a Old Trafford.

Man United za ta kammala wasan karshe a shekarar 2023 ranar Asabar 30 ga watan Disamba da zuwa gidan Nottingham Forest.

Leave a comment