Afcon 2023 Ivory Coast: An fitar da sunayen rafli babu daga Nigeria

Hukumar kwallon kafa ra Afirka, Caf ta fitar da sunayen wadanda za suyi alkalancin gasar kofin Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.

An bayyana mutum 68 da za su gudanar da aiki daga wasu kasashe a Afirka, wadanda suka yi fice a busa wasannin gasar nahiyar.

Cikin alkalan guda 26 ne za su aikin rafli da 30 mataimaka da 12 da za su kula da VAR a fafatawar da za a fara daga 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu.

Sai dai babu rafli ko daya daga Nigeria, amma an gayyato daga Algeria da Kenya da Ethiopia da Congo da Mali da kuma Chad.

Sauran sun hada daga kasar Mauritius da Burundi da Djibouti da Lesotho da Somali da Benin Republic da Madagascar da kuma Sao Tome and Principe.

Ana sa ran wadanda aka bai wa goron gayyata za su je ranar 5 ga watan Janairu, domin karbar horo kafin fara wasannin.

Latsa nan kaga alkalan da aka gayyata list-afcon-2023-selected-referees-2.pdf

Leave a comment