Welch ta zama macen farko da ta busa gasar Premier League a tarihi

Rebecca Welch ta zama mace ta farko da ta yi rafli a gasar Premier League wasan Fulham da Burnley a Craven Cottage ranar Asabar.

Welch, mai shekara 40 daga Washinghton da ke Arewacin England tana aiki a hukumar lafiya ta fara rafli a matakin sana’a a 2010.

A shekarar 2021 ta zama ta farko da ta yi alkalancin tamaula a English Football League a karawar ‘yan rukuni na hudu tsakanin Harrogate da Port Vale.

Haka kuma Welch ita ce macen farko da ta busa Championship da fafatawar zagaye na uku a FA Cup.

A watan jiya ta zama ta farko da ta yi alkalanci a Premier League a matakin kar-ta-kwana a wasan Fulham da Manchester United.

Welch ta goge a alkalancin kwallon kafa, wadda ta busa manyan wasanni da yawa har da gasar cin kofin duniya ta mata a 2023 da aka yi a Australia da New Zealand.

Leave a comment