Manchester City ta zama ta farko da ta ci kofi biyar a Ingila a shekara

Manchester City ta dauki kofin duniya na zakarun nahiyoyi, bayan da ta doke Fluminense ta Brazil 4-0 a Saudi Arabia.

Minti daya da take leda Man City ta ci kwallo ta hannun Julian Alvarez daga nan Fluminense ta ci gida ta hannun Nino.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu City ta ci gaba da zura kwallaye a raga ta hannun Phil Foden da kuma Julian Alvarez.

Man City ta buga wasan ne bayan ita take da Champions League na Turai, Fluminense tana da kofin zakarun Kudancin Amurka duk da suka lashe a bara.

Wannan nasarar da Man City ta yi ta bi sawun Manchester United da Liverpool da kuma Chelsea a jerin wadanda suka lashe Fifa Club World Cup a Ingila.

To sai dai kungiyar ta Etihad ta zama ta farko da ta dauki kofi biyar a shekara daya, wadda ta lashe Premier League da FA Cup da Champions League a bara da kuma Uefa Super Cup cikin watan Agusta duk a shekarar 2023.

Wasan neman mataki na uku kuwa a ranar ta Juma’a Al Ahly ta Masar ce ta doke Urawa Red Diamonds ta Japan da cin 4-2.

Leave a comment