Real Madrid ta koma ta daya a teburin La Liga

Real Madrid ta dare matakin farko a teburin La Liga, bayan da ta je ta ci Deportivo Alaves 1-0 a wasan mako na 18.

Real ta ci kwallon ta hannun Lucas Vazquez daf da lokaci zai cika na minti 90.

Sai dai Real ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Nacho Fernandez jan kati.

Da wannan sakamakon Real ta hada maki 45 ta koma ta daya, amma iri da na Girona, wadda ta je ta tashi kunnen doki 1-1 a gidan Real Betis.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a jiyan Cadiz da Real Sociedad suka yi kurman duro da wanda Real Mallorca ta ci Osasuna 3-2.

Sai a ranar Asabar za a kammala wasan mako na 18 tsakanin Atletico Madrid da Sevilla.

Daga nan aje hutun Kirsimite sai biyu ga watan watan Janairun badi a koma fagen daga.

Leave a comment