Mbappe ya ci kwallo a ranar cikar shekarar haihuwarsa

Kylian Mbappe ya ci kwallo a ranar bikin haihuwarsa shekara 25, bayan da Paris Saint-Germain ta doke Metz 3-1 a Ligue 1 ranar Laraba.

Da wannan sakamakon PSG, wadda take ta daya ta bayar da tazarar maki biyar a teburin Ligue 1.

Vitinha ne ya fara ci wa PSG kwallo a zagaye na biyu a Parc des Princes, sai kuma Mbappe ya kara na biyu.

Matthieu Udol ne ya zare daya daga baya Mbappe ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a fafatawar.

Haka kuma dan uwan Mbappe, Etan mai shekara 16 ya shiga wasan a karon farko da ya yi wa PSG tamaula.

Kenan PSG ta kammala wasan 2023 da tazarar maki biyar tsakaninta da Nice, wadda ta ci Lens 2-0 ranar Laraba, kuma dan wasan Nigerian, Terem Moffi ya ci kwallayen.

Monaco, wadda take ta ukun teburi, wadda ta doke Toulouse 2-1 tana da tazarar maki bakwai tsakaninta da PSG.

Ita kuwa Lyon ta bar gurbin ‘yan ukun karshen teburi, bayan da ta ci Nates 1-0, kuma kyaftin Alexandre Lacazette ne ya ci kwallon.

Leave a comment