Carabao Cup: Liverpool da Fulham Chelsea da boro

Liverpool za ta kara da Fulham, Chelsea da Middlesbrough a wasan daf da karshe a Carabao Cup da aka raba jadawali a jiya Laraba.

A jiya Liverpool ta dura kwallo 5-1 a ragar West Ham, Fulham kuwa doke Everton ta yi a bugun fenariti a Godison Park.

Chelsea ma a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta kai wannan matakin bayan nasara a kan Newcastle United ranar Talata.

Ita kuwa Middlesbrough doke Porte Vale 3-0 ta yi kamar yadda ta yi mata a wasan karshe a 1998.

Za a buga daf da karshe gida da waje a Carabao Cup ranar 8 a kuma yi wasa na biyu ranar 22 ga watan Janairun 2024.

Jadawalin Carabao Cup:

Liverpool da Fulham

Middlesbrough da Chelsea

Leave a comment