Barcelona ta yi nasara a kan Almeria da ci 3-2 a wasan mako na 18 a gasar LaLiga ranar Alhamis.
Barcelona ta ci kwallayen ta hannun Raphinha da kuma Sergi Roberto da ya zura biyu a raga.
Ita kuwa Almeria ta ci kwalayen ta hannun Leo Baptistao da kuma Edgar Gonzalez Estrada.
Da wannan sakamakon Barcelona ta koma mataki na uku a teburin La Liga da maki 38, Atletico ta koma ta hudu da maki 35.
Girona ce ta daya a kan teburi da maki 44, sai Real Madrid ta biyu mai maki 42.
Za a ci gaba da wasannin mako na 18 ranar Alhamis:
- Real Betis da Girona
- Cadiz da Real Sociedad
- Deportivo Alaves da Real Madrid
- Real Mallorca da Osasuna