Abinda ya kamata ku sani kan wasan Barcelona da Almeria

Almeria ta ziyarci Barcelona, domin buga wasan mako na 18 a gasar La Liga ranar Laraba.

Wanann shi ne wasa na 18 da za su fafata a tsakaninsu a dukkan karawa, inda Barcelona ta ci 14 da canjaras biyu, Almeria ta yi nasara a daya.

Ciki har da nasara 11 da Barcelona ta yi a LaLiga da canjaras biyu da Almeria ta ci daya, yayin da kungiyar Camp Nou ta lashe wasa uku da suka hadu a kofi.

Sun kakar a bara sau biyu, inda Barcelona ta ci 2-0 ranar 5 ga watan Nuwambar 2022 a La Liga.

A wasa na biyu kuwa shi ne Almeria ta yi nasarar cin 1-0 ranar 26 ga watan Fabrairun 2023.

Barcelona tana mataki na hudu a kan teburin La Liga da maki 35, iri daya da na Atletico Madrid ta hudu.

Girona ce ta daya mai maki 44, sai kuma Real Madrid ta biyu da makinta 42.

Wasannin da za a buga ranar Laraba:

  • Barcelona da Almeria     
  • Athletic de Bilbao da Las Palmas    
  • Villarreal da Celta de Vigo      

Leave a comment