Alava ya ji mummunan rauni a gwiwa

Mai tsaron bayan Real Madrid, David Alaba ya ji mummunan rauni kamar yadda kungiyar ta sanar.

Ranar Lahadi da yammci kungiyar da ke Santiago Bernabeu ta sanar cewar ‘’Alaba ya ji rauni a gwiwarsa ta hagu, za kuma a yi masa gwaje-gwaje.’’

Wakila kenan dan kwallon ya gama buga wasannin kakar bana, ana cewa da kyar idan zai iya buga Euro 2024 da za a yi a Jamus tsakanin Yuni zuwa Yuli.

Alaba ya ji rauni ne a wasan da Real Madrid ta doke Villareal 4-1 ranar Lahadi a gasar La Liga mako na 17.

Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Girona ta biyu.

Ko da yake Girona za ta iya komawa kan matakin farko da zarar ta doke Alaves a wasan da za su buga ranar Litinin.

Leave a comment